5 Satumba 2020 - 11:54
Hukumar Lafiya Ta Duniya Zata Ware Alluran Ragakafin Covid 19 Miliyan 230 Na Farko Ga Nahiyar Afirka

Hukumar lafiya ta duniya ta bada sanarwan cewa zata ware alluran riga kafin cutar korona miliyan 230 ga kasashen Afrika idan an samar da allura biliyon 2 na farko a duniya a karshen shekara ta 2021 mai zuwa.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters daga birni Nairobi inda ofishin hukumar reshen nahiyar Afrika ya ke, ya kara da cewa idan an samar da alluran sai har yi gwajinsa a nahiyar ta Afirka kafin a fara yi wa mutane.

Reuters ya nakalto Richard Mihigo shugaban hukumar ta WHO a nahiyar Afirka ya na fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa wannan adadin shi ne kashi 20% na yawan mutanen Afirka, sannan za’a fara yiwa jami’an kiwon lafiya alluran riga kafin don su ne a gaba-gaba wajen yaki da cutar, sannan a fara yi wa sauran mutane.

Labarin ya kammala da cewa ya zuwa yanzu dai alluran guda biyu ne kawai aka fara gwajinsu a nahiyar afirka.

342/