2 Satumba 2020 - 09:45
An Kama Mayakan ‘Yan Ta’adda Na Kungiyar Daesh 12 A Lardin Ambar Na Kasar Iraqi

Ma’aikatar ‘yansandan ciki, na kasar Iraqi ta bada sanarwan cewa jami’an tsaron kasar sun kama mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh su 12 a Lardin Ambar na yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran ABNA24 na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar ta Iraqi ta na fadar haka a jiya Litanin, ta kuma kara da cewa:

“Wadanda aka kama, sun arce daga kasar ta Iraqi zawa wata kasa makobciyar kasar, bayan da jami’an tsaron kasar suka kwaci iko da Lardin a shekara ta 2017, amma suka sake dawowa don aiwatar da ayyukan ta’addanci”.

Labarin ya kara da cewa jami’an tsaro a lardin na Ambar sun gano rumbun ajiyar makamai da kayakin aikin soja, na mayakan, wadanda suka hada da, manya-manyan bindigogi, damarar kunan bakin wake, makamai masu linzami samfurin katusha, makamin harba rokoki da kayakin aikin soja da dama.

342/