1 Satumba 2020 - 10:32
​Rauhani: Kyautata Alaka Da Kasashe Makwabta Shi Ne Kan Gaba A Siyasar Kasar Iran

<p "="">Shugaban kasar Iran Dr. Sheikh Hassan Rauhani ya bayyana cewa, daya daga cikin muhimman lamurra a siyasar kasarsa shi ne kyautata alaka da kasashe makwabta.

ABNA24 : A lokacin da yake jagorantar zaman majalisar ministocin kasar Iran a yammacin jiya a birnin Tehran, shugaba Rauhani ya jaddada matsayin gwamnatin kasarsa na ci gaba da siyasar kyautawa da kuma karfafa alaka da dukkanin kasashe makwabta.

Ya ce alaka tsakanin kasashen yankin alaka ce ta tarihi, wadda take komawa ga dubban shekaru, wanda kuma babban burin makiya al’ummar yankin ita ce wargaza wannan alaka da ‘yan uwantaka da ke tsakanin al’ummomin yankin gabas ta tsakiya.

Rauhani ya kara jaddada cewa ma’aikatar harkokin wajen kasar za ta ci gaba da bin salon karfafa wannan alaka tare da dukkanin kasashen yankin, ta fuskokin siyasa, tattalin arziki, cinikayya, ayyukan hadin gwiwa a bangaren bincike na ilimi, noma, makamashi, karfin wutar lantarki da sauransu.

Yanzu haka dai akwai kasashe da dama na yankin da suke da alaka mai karfi ta fuskoki tattalin arziki da cinikayya tare da Iran, da suka hada da Iraki, Qatar, Oman, Kuwait, Lebanon da sauransu.

342/