ABNA24 : Fira ministan gwamnatin ta Sudan, Abdallah Hamdok, ya ce gwamnatin wucin gadin ba ta da hurimin yanke shawara kan kulla akala da Is’raila.
Wannan bayannin dai na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ke wata ziyara a kasar ta Sudan, bayan wacce ya kai a Isra’ila.
Ziyarar ta Pompeo ita ce irinta ta farko ta wani babban jami’in Amurka a kasar ta Sudan a cikin shekaru 15 da suka gabata.
A baya baya nan dai Amurka na kokarin ganin ta kulla alaka tsakanin kasashen Larabawa da Isra’ila, bayan wacce ta jagoranta tsakanin mahukuntan yahudawan sahayoniya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa a baya baya nan.
342/