24 Agusta 2020 - 14:55
Bore Ya Yi Ajalin Fursuna 20 A Madagaska

Hukumomin shari’a a Madagaska, sun bayyana cewa fursunoni ashirin ne suka rasa rayukansu yayin wani hargitsi a wani gidan yari dake kudu maso gabashin kasar.

ABNA24 : Lamarin dai ya faru ne wannan Lahadin a gidan yarin na Farafangana, bayan da wasu gomman fursunoni suka tada bore a gidan yarin.

Sanarwar da ma’aikatar shari’a ta kasar ta fitar ta ce fursunonin sun aukawa masu gadin gidan yarin suka kuma kwace wata bindiga, lamarinda da ya yi sanadin mutuwar fursuna 20 da kuma jikkata wasu 8.

Baya ga hakan kuma akwai fursunoni 68 da suka arce daga gidan yarin, koda yake a cewar sanarwar an cafko 37 daga cikinsu.

Tuni dai aka karfafa matakan tsaro a gidan yarin yankin, inji hukumomnin kasar.

342/