A farkon watan Agustan nan ne wani kwamiti majalisar dokokin kasar da aka kafa a watan Janairu, ya mika wa kotu rahoton wani bincike da ya yi kan yadda Mohamed Ould Abdel Aziz, ya tafiyar da mulkin kasar.
Wata majiya a majalisar dokokin kasar ta ce shaidawa masu aiko da rahotanni cewa, Daga cikin binkiken da akayi har da yadda ya tafiyarda wasu harkoki, da suka shafi kudaden shiga na man fetur, da sayar da filayen gwamnati A Nouakchott, da kuma saida wani kamfanin shigar da kayan abinci na kasar da kuma ayyukan wani kamfanin kamun kifi mallakin kasar China a kasar.
342/