ABNA24 : Tasahar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a yammacin jiya sojojin Isra’ila sun yi amfani da harsashin bindiga wajen harbe wani matashi musulmi dan shekaru 19 da haihuwa a kusa da masallacin Quds, inda suka hana jama’a isa wurinsa har said a suka tabbatar da ya mutu.
Sojojin na Isra’ila sun yi da’awar cewa matashin ya yi yunkurin daba ma wani daga cikinsu wuka ne, amma ba tare da sun yi nuna wata hujja da ke tabbatar da hakan ba, inda sau tari sukan bindige Falastinawa bisa hujjar cewa Falastinawa na shirin daba musu wuka ne.
Ko a jiya sojojin Isra’ila sun harbi wani tsoho musulmi dan shekaru 60 a cikin birnin na Quds bisa hujjar cewa zai daba musu wuka, bayan harbinsa kuma ta bayyana cewa kurma ne wanda bai ma san abin sojojin yahudawan suke ciki ba.
A cikin lokutan baya-bayan nan dai Isra’ila ta tsananta ayyukanta na cin zarafin al’ummar Falastinu, a cikin birnin Quds da sauran yankunan yammacin kogin Jordan.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin sarakunan larabawan yankin tekun fasha ke ta hankoron ganin sun kulla alaka ta diflomasiyya da Isar’ila, ba tare da nuna takaici kan abin da take aikatawa a kan musulmin Falastinu ba.
342/