17 Agusta 2020 - 10:25
Iran Tana Shawartar UAE Da Ta Sake Nazari Akan Kulla Alaka Da Makiya

Janar Bakiry, wanda shi ne babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran, ya yi kira ga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da ta sake yin nazari akan matakin da ta dauka na kulla alaka da HKI, tun kafin lokaci ya kure.

ABNA24 : A wani taron fahimtar juna da aka yi a tsakanin sojoji da kuma gidan talabijin da Radio na Iran a yau Lahadi, janar Bakiry ya yi ishara da abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya, sannan ya ce; Abinda ya faru a tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da Haramtacciyar Kasar Isra’ila babban bala’i ne, mai cike da abin takaici.”

Janar Bakiry ya kara da cewa; Shakka babu, halayyar al’ummar Iran da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa za ta sauya, kuma za ta dauki mataki matukar aka cutar da tsaron kasarta.

342/