16 Agusta 2020 - 10:27
Lebanon : Binciken Musababbin Fashewar Beirut Zai Dau Lokaci

Shugaban kasar Lebanon, Michel Aoun, ya bayyana cewa binciken da ake kan musababbin fashewar data auku a tashar ruwan Beirut zai dau lokaci.

ABNA24 : A wata hira da tashar talabijin din faransa ta BFM TV, shugaba Aoun, ya ce bisa ga dukkan alamu ba za’a kammala binciken ba cikin sauri.

Shugaban ya kuma yi alakwarin cewa tallafain da kasashen duniya suka bayar zai isa hannun wadanda akayi dominsu.

Ya kara da cewa binciken da ake ba na kasa da kasa ne ba, kawai yana samun taimakon kasashen duniya.

Kasashen duniya dai na ci gaba da matsin lamba wa kasar ta Lebanon akan ta gaggauta gudanar da bincike kan musababbin faruwar fashewar data auku ranar 4 ga watan Agustan nan wacce kuma ta yi sanadin mutuwar mutane 172, da kuma jikkata wasu sama da 6,500 da kuma hadassa barna mai yawa a Beirut babban birnin kasar.

342/