ABNA24 : Jaridar “Yedioth Ahronoth” da ake bugawa da harshen Hebrew ta ambaci cewa soja guda na ‘yan sahayoniyar ya jikkata a lokacin da suke kashe gobarar da ta tashi a yankunanda suke iyaka da yankin Kisofim da ke kan iyaka da Gaza.
A yau Laraba ma dai wata gobarar ta tashi a yankunan da su ke kan iyaka da Gaza. “Yan sahayoniya kan yi zargin cewa Palasdinawa ne su ke turo balo-balo mai dauke da abubuwa masu zafi da suke haddasa tashin gobara a yankin.
Tashar talabijin ta “Channel 7” ta yahudawan Sahayoniya ta bayar da labarin cewa da safiyar yau an sami tashin gobara a wurare bakwai.
342/