6 Agusta 2020 - 12:15
DRC : Mutum 1,300 ‘Yan Bindiga Suka Kashe Cikin Wata Shida

Majalisar Dinkin Duniya, ta fitar da wani rahoto dake cewa sama da mutum 1,300 ne gungun masu dauke da makamai suka kashe a cikin watanni shidan farko na shekara 2020 din nan a jamhuriyar Demokuradiyar Congo.

ABNA24 : Wannan adadin a cewar MDD, ya linka sau uku idan aka kwatanta da shekara 2019 data gabata a daidai wannan lokaci.

Rahoton da ofishin kare hakkin dan adam na MDD, ya fitar, ya ce a tsakanain watan janairu zuwa Yuni na bana, mayaka daga gungu daban daban sun hallaka akalla mutum 1,315 wadanda suka hada da mata 267 da kuma yara 165.

Wannan a cewar ofishin na (BCNUDH), ya nuna yadda al’amuran kare hakkin dan adam suka kara kazancewa a yankunan dake fama da rikici a wannan kasa ta Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, da suka hada da Ituri, da kudanci da kuma arewacin Kivu, da Tanganyika.

Tashe tashen da suke faruwa a yankunan sun hada da rikicin kabilanci da kuma na tsakanin gungun kungiyoyi masu dauke da makamai, wanda ya tilastawa sojojin R.D Congo, kaddamar da farmaki kan dukkan bangarorin, amma duk da hakan ana ci gaba da samun kashe kashen fararen hula, koda yake daga bangaren sojojin gwamnati an samu raguwar cin zarafi da kashi (-3%).

342/