5 Agusta 2020 - 12:43
Rouhani: Makiya Suna Amfani Da Yakin Farfaganda Don Nuna Gazawar Gwamnatin Kasar Iran

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa, bayan gazawa wajen cimma burinsu na durkusar da tattalin arzikin kasar Iran ta hanyar takunkuman tattalin arziki mafi tsanani, makiya sun dawo kan yakin farfaganda, don nuna gazawar gwamnatin kasar wajen aiki wa mutanen kasar.

ABNA24 : Shugaban ya kara da cewa tuni makiya su na sauya gaskiya dangane da ayyukan da gwamnatin kasar Iran takewa mutanen kasar don cimma wannan manufar. Rouhani ya bayyana haka ne a safiyar yau Talata, a lokacinda yake shugabantar taron majalisar tattalin arzikin kasar a nan birnin Tehran.

Shugaban ya ce Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi sayyeed Aliyul Khamina’ii ya bayyana shirye-shiryen makiya na durkusar da tattalin arzikin kasar Iran, na karami da dogon ango, a cikin jawabnsa na baya-bayan nan, daga cikin har da yakin farfaganda don hana tattalin arzikin kasar ci gaba. Sannan da boye gaskiyar abinda yake faruwa a kasar. Daga karshe shugaban ya ce wadannan shirye-shirye biyu suna tafiya tare.

342/