ABNA: Fadar White House ta ce dokar umarnin shugaban kasar zata taimaka wurin haramtawa ma’aikatun gwamnati maye gurbin Amurkawa ma’aikata ba bisa ka’ida ba da ‘yan kasar waje don neman rahusa.
Dokar ta bukaci duk ma’aikatun gwamnati su kamala bincike su nuna ko suna daukar ‘yan asalin Amurka da ‘yan kasa aiki a kan mukaman aiki da mutane da dama ke nema.
Trump ya fadawa manema labarai a jiya Litnin cewa zai kori shugaban ma’aikatar TVA saboda yana daukar ‘yan kasar waje kuma yana daukar albashi mai yawa.
342/