ABNA: Bayanai sun ce zanga zangar ta jiya ita ce mafi girma inda mutane sama da 10,000 suka taru a gaban gidan Netanyahun, a birnin tel Aviv, suna masu bukatar sa ya yi murabus daga mulki.
An dai shafe makwanni ana irin wannan zanga zanga kan yadda Netanyahun ke tafiyar da harkokin siyasar yahudawan da yaki da cutar kotona da kuma tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa.
342/