ABNA24: A gefe daya Fira ministan kasar ta Lebanon Dr. Hassan Diyab, ya bayyana harin da HKI ta kai wa Lebanon da cewa wani yunkuri ne na yin matsin lamba domin shigar da sauye-sauye a cikin ayyukan dakarun MDD na, ( UNifil ) da suke aiki a kasar.
Bugu da kari Fira ministan na kasar Lebanon ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta yi tir da harin da HKI ta kai wa Lebanon, da kuma tilasta mata aiki da kuduri mai lamba 1701.
Majalisar Ministocin kasar ta Lebanon ta dorawa ministan harkokin waje nauyin kai karar HKI a gaban Majalisar Dinkin Duniya saboda hare-haren day akin kudancin kasar kwanaki biyu da su ka gabata.
342/