28 Yuli 2020 - 11:37
Yemen: Yara Shida Ne Suka Mutu Ko Suka Ji Rauni Sanadiyyar Fashewar Bom A Maarab

Akalla yara kanana hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu da kuma biyu wadanada suka ji rauni sanadiyyar fashewar bom a wani wuri a cikin lardin Maarab na kasar Yemen.

ABNA24: Tashar talabijin ta Almasiri ta bayyana cewa bon din na irin wadanda jiagen saudia da kawayenta suke jafawa kan mutane wadanda basu tashi ba, amma a lokacinda yaran nan suka taba shi sai ya feshe ya kuma kashe su.

Har’ila yau a wani rahoton jiragen yakin saudiya da kawayenta sun zafafa kai hare-hare a yankin Hudaida a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudiya take jagorantan wasu kasashen larabawa, daga cikin har da gwamnatin Hadaddiyar daular Larabawa, kai hare-hare kan gwamnatin kasar Yemen da nufin maida tsohon shugsban kasar wato Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar.

342/