24 Yuli 2020 - 14:37
Sojojin Amurka Sun Taka Rawa Wajen Yaduwar Corona A Cikin Kasar

Kafafen watsa labarun Amurka sun bayyana cewa,kasar tana da sojojin a girke a cikin gwamman kasashen duniya, kuma masu yawa daga cikinsu sun kamu da cutar corona.

ABNA24: Rahoton ya bayyana cewa; Sojojin Amurka ne tushe na farko na yaduwar cutar corona, domin tun a cikin watan Aprilu, adadin da ya kai 20,000 na sojojin sun kamu da cutar ta lumfashi.

Jaridar Newyork Times ta ce da akwai dalilai masu karfi da suke tabbatar da cewa, sojojin Amurka suna taka rawa wajen yaduwar cutar ta corona.

Har ila yau rahoton ya ce; yanayin yadda sojojin su ke rayuwa a cikin barikokinsu a Georgia da California cikin cakudawa da juna da yadda ake basu horo, haka nan yanayin zamansu a cikin gidajen holewa, suna a matsayin yanayi mafi dacewa na yaduwar corona.

342/