ABNA24: An dai dage shari’ar ce awa guda bayan soma ta saboda rashin isashen wuri a cikin farfajiyar kotun.
A jiya ne hambararen shugaban kasar ya sake bayyana a gaban kotun Khartoum, a wannan karo kuwa bisa tuhumarsa da kwace mulki ta hanyar amfani da tsinin bindiga shekaru 31 da suka gabata.
A ranar 30 ga watan Yunin shekara 1989 ne, Al’Bashir ya kifar da gwamnatin Sadek el-Madhi.
Baya ga Al’bashir din da akwai wasu tsafin jami’an gwamnati da manyan sojoji 27 da su ma ake ma irin wannan tuhuma.
342/