21 Yuli 2020 - 12:54
Sakamakon Gwajin Alluran Riga Kafin Corona Na Farko Ya Tabbatar Da Ingancinsa

Sakamakon gwaji na farko da aka yi na alluran riga kafin cutar Korona ko Covid 19 a kasar Britaniya ya tabbatar da ingancinta.

ABNA24: Tashar talabijin ta Sky News Arabiyya ya nakalto kamfanin dillancin labaran reuters yana cewa sakamakon gwajin na alluran riga kafin mai suna “AZD1222 a kan jikunan mutanen da aka yi gyajin a jikunansu ya nuna cewa alluran tana samar da kariyar da ake bukata na yaki da cutar da kuma kare mutum daga kamuwa da ita.

Banda haka sakamakon ya nuna cewa babu wata illa da aka gano ya zuwa yanzu ga wadanda aka yiwa alluran.

Labarin ya kara da cewa kamfanin samar da magunguna na Astra-Zeneca PLC na kasar Britaniya ya na aiki da tare da masana a jimi’ar Oxford don kara ingancin allura.

Tashar talabijin ta Sky News ta nakalto wani daga cikin kwararru a jami’ar Oxford wadanda suke aikin samar da alluran yana cewa, indan babu wata matsala da ta bijoro nan gaba, akwai fatan cewa alluran za ta fito nan da watan satumba na wannan shekara.

342/