ABNA24: An dai kwashe tsawon watanni hudu a jere ana tattaunawa kan wannan batu, amma ba tare da samun daidaiton baki tsakanin kasashe mambobi na kugiyar tarayyar turai ba, wanda sai a yau ne shugabannin kasashen tarayyar turan suka cimma matsaya kan batun.
Bayan shafe kwanaki 4 cur ana tafka mahawara kan yadda za a rarraba kudin tallafin farfado da tattalin arzikin da coronavirus ta kassara, shugabannin kasashen Turai sun cimma matsaya a safiyar yau Talata.
Kudin da aka amince kan rarraba su tsakanin kasashe mambobin kungiyar ya kai euro biliyan 750, duk da cewa wasu daga cikin kasashen ne za su fi samun kaso mai yawa saboda yadda annobar corona ta kassara tattalin arzikinsu.
Kasashen Jamus da faransa ne dai kan gaba wajen goyon bayan wannan shiri, wanda ake ganin zai taimaka wajen rage matsaloli da dama da al’ummomin kasashen turai suka fada a cikin wannan lokaci saboda cutar corona.
342/