ABNA24: Masu zanga zangar na kuma nuna dawa da abunda suka danganta da matsin tattalin arziki da kuma yadda gwamnati ke tafiyar da sha’anin yaki da annobar korona wanda ya jefa al’umma cikin kangin rayuwa.
A birnin Kudus daruruwan mutane ne suka taru a kofar gidan Netanyahu, suna masu kiran ya sauka daga kan kujerarsa.
Daga bisani dai zanga zanga ta rikide zuwa tarzoma bayan da 'yan sanda suka 'yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi, domin tarwatsa dubunnan masu zanga-zangar.
A wani lakoci yau Lahadi ne ake sa ran sake komawa shari’a da ake wa firai ministan Isra’ilar, Benjamen Netanyahu, kan zargin cin hanci da rashawa da cin amana.
342/