(ABNA24.com) Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto Bahram Qasimi jakadan kasar Iran yana fadar haka a dai-dai lokacinda yarjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran take cika shekaru 5 da kullawa.
Qasimi ya kara da cewa Iran ta shiga tattaunawa da manya-manyan kasashen duniya dangane da shirin nukliyar kasar shekaru 13 kafin a cimma yarjejeniyar a shekara ta 2015. Amma tun farkon yarjejeniyar Amurka ce ta fara sabawa yarjejeniyar, kafin gwamnatin Amurka ta yanzu ta fice daga yarjejeniyar A shekara ta 2018.
Daga karshe jakadan ya kammala da cewa idan har dukkan kasashen da suka rattabawa yarjejeniyar hannu suka juya mata baya to Iran ba za ta zama ita kadai ce mai mutuntata ba.
342/