13 Yuli 2020 - 11:40
A kowace Rana Ta Allah, Iran Tana Kera Takunkumin Rufe Fuska Miliyan 6.5

Mataimakin ministan masana’antu na iran Mehdi Sadeki Niaraki ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Irna cewa; Iran din tana kera takunkumin rufe fuska da hanci domin fada da cutar corona da ya kai miliyan 6 da rabi

(ABNA24.com) Har ila yau, mataimakin ministan masana’antun na Iran ya kara da cewa; A Iran ba a karancin man wanke hannu da ake amfani da shi, haka nan dukkanin sauran kayayyakin fada da cutar ta lumfashi.

Sadeki Niaraki ya kara da cewa; Gabanin bullar cutar corona adadin takunkumin da ake kerawa a Iran a kowace rana, bai wuce 200,000, amma yanzu ya rubanya har sau 3000%

Har ila yau mataimakin ministan masana’antun na Iran ta ce; idan za kirga da takunkumin da masu zaman kansu da masu sa-kai suke samarwa to adadin ya dara miliyan 6 da rabi.

342/