10 Yuli 2020 - 14:32
A Kalla Mutane 7 Ne Su Ka Mutu Sanadiyyar Fashewar Wasu Abubuwa A Reshen kamfanin NNPC Da Ke Jahar Rivers A Najeriya

Kamfanin man fetur din na Najeriya ( NNPC) ne ya sanar da cewa mutane 7 ne su ka rasa rayukansu saboda fashewar wasu abubwa a Gbetiokun.

(ABNA24.com)  Sanarwar ta fito ne ta hannun Dr. Kennie Obateru wanda shi ne kakakin bangarin gudanar da ayyuka na banagren NPDC dake karkashin kamfanin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa an sami hatsarin ne a lokacin da ake kafa wani tsani a ranar Talata a cibiyar kamfanin da ke Benin Jahar Rivers, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane 7.

Tuni dai kamfanin ya sanar da bude bincike akan musabbabin mutuwar mutanen.

Tuni dai babban manajan kamfanin Malam Mele Kyari ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su.

342/