(ABNA24.com) A lokacin da yake zantawa da shugaba gami da mambobin kwamitin bunkasa harkokin tattalin arziki na kasa a birnin Tehran, mataimakin shugaban kasar Iran Ishaq Jahangiri ya bayyana cewa, babban abin da Amurka ta sanya a gaba a halin yanzu shi ne ganin bayan tattalin arzikin kasar ta Iran.
Ya ce Amurka ta kara tsananta wannan mataki ne a daidai lokacin da kasar take fuskantar zaben shugaban kasa nan da ‘yan watanni masu zuwa, da nufin tilasta Iran din ta mika wuya, ta yadda hakan zai zama daya daga cikin muhimman makamai siyasa da gwamnati mai ci a kasar ta Amurka za ta yi amfani da su domin neman kuri’a.
Jahangiri ya ce kasarsa tana matakai daban-daban da take dauka domin rage kaifin matsin lambar Amurka a kan tattalin arzikinta, mafi muhimmanci daga ciki kuwa shi ne daina dogaro da danyen man fetur da dangoginsa da kasar tak efitarwa, tare da ci gaba da bunkasa wasu harkokin samun kudaden shiga wadanda ba na man fetur ba, wanda ya ce tuni sun yi nisa a cikin wannan shiri.
342/