(ABNA24.com) Wannan dai a cewar Zhang Jun, wanda ke yabawa da matakin, wata alama ce ta nuna cewa China na shirye wajen son hadin kan duniya.
Kuma hakan a cewarsa ya nuna yunkurin China na mutunta cinikin makamai.
Hakan dai na nuna China zata sayar da makamai ne kawai ga kasashe masu ‘yancin kansu ba wai wasu bangarori masu zaman kansu ba.
China dai ita kasa ta biyu a duniya wajen kera makamai, kuma yanzu ita kasa ta 107 data sanya hannu kan yarjejeniyar ta MDD, da aka cimm a ashekara 2013, wacce ta tanadi ko wacce kasa ta fayace duk wani irin ciniki na makamman da take kerawa domin kada su fada hannun miyagun kungiyoyi.
342/