4 Yuli 2020 - 11:30
Kamaru : An Fara Tattaunawa Tsakanin Gwamanati Da ‘Yan A Ware

Bayanai daga Jamhuriyar Kamaru na cewa, an fara tattaunawa tsakanin gwamnatin da masu fafatukar a ware na yankunan masu magana da turancin Ingilishi a yammacin kasar.

ABNA24: Ko da yake dai gwamnatin kasar bata so yin bayyani ba kan batun, amma wasu majiyoyi sun ce bangarorin na tattaunawa a Yaoude kan batun tsagaita wuta

Wannan shi ne karon farko da bangarorin suka zauna kan teburin tattaunawa a cikin shekaru uku na fadan da sojojin kasar ke gwabzawa da kungiyoyin masu fafatukar a ware.

Shi ma wani babban jami’in MDD, wanda bai so a ambaci sunansa bay a tattabarwa da kamfanin dilancin labaren AFP, da tattaunawar, kamar yadda wani jagoran ‘yan fafatukar a waren shi ma ya tabbatar, inda suka gana da wasu jamia’n gwamnati.

Tun bayan barkewar rikicin kasar ta Kamaru, mutane sama da 3,000 ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 700,000 suka tsare daga muhallensu a cewar kungiyoyin kasa da kasa.

342/