30 Yuni 2020 - 09:18
​Iran: Kotu Ta Bayar Da Sammacin Kamo Donald Trump

Kotun kasar Iran ta bayar da sammacin damko wasu jami’an gwamnatin Amurka su 36 da suke da hannu wajen kisan Janar Qasem Sulaimani , da cikinsu har da shugaban kasar ta Amurka Donald Trump.

(ABNA24.com)  Kotun kasar Iran ta bayar da sammacin damko wasu jami’an gwamnatin Amurka su 36 da suke da hannu wajen kisan Janar Qasem Sulaimani , da cikinsu har da shugaban kasar ta Amurka Donald Trump.

A zaman da manyan jami’ai a ma’aikatar shari’a ta kasar Iran suka gudanar, babban mai shigar da kara na kasar ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu sun iya gano mutane 36 da suke da hannu a kisan Janar Qasem Sulaimani, wadanda dukkaninsu jami’ai na sojoji da siyasa a kasar Amurka.

A cikin umarnin da kotun kasar ta Iran ta bayar a yau, ta bukaci da a kamo wadannan mutane, daga cikinsu har da shugaban kasar Amurka Donald Trump a mika mata su, domin su fuskanci hukunci na shari’a.

Baya ga haka kuma kotun ta mika wannan sammaci ga hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol, domin ta taimaka wajen kame wadannan jami’ai na Amurka da ake zarginsu da aikata laifin kisan kai da kuma ta’addanci.


/129