(ABNA24.com) A cikin jawabin rantsar da shi, M. Chakwara, ya yi alkawarin sauke yaunin da ya rataya kansa a matsayin shugaban kasa da kuma kare kundin tsarin mulkin kasar.
Sabon hsugaban, ya kuma sha alwashin yin aiki tukuri wajen ciyar da kasar, da kuma zama shugaba na kowa, har ma wadanda basu zabe shi ba.
M. Chakwera, ya kada shugaban kasar mai barin gado, Peter Mutharika, a zaben shugabancin kasar na biyu da aka gudanar, bayan da shugaba Mutharika ya ki amince shan kayi a waccen zaben na watan Mayun 2019, bisa zargin da ya yi na cewa an tabaka magudi.
A sakamakon zaben data fitar, hukumar zaben kasar ta ce M. Chakwera, dan shekaru 67, wanda tsohon fasto ne ya lashe zaben da kashi 58,57% ya yawan kuri’un da aka kada, saidai jam’iyya mai mulki ta sake yin fatali da sakamakon zaben.
Malawi, ta zama kasa ta biyu a yankin kasashen Afrika dake kudu da hamadar sahara inda aka soke zaben shugaban kasa, bayan Kasar Kenya a shekara 2017.
/129
29 Yuni 2020 - 07:03
Lambar labari: 1051190
Madugun ‘yan adawa na Malawi, Lazarus Chakwera, ya yi rantsuwar kama mulki yau, a matsayin sabon shugaban kasar, kwana guda bayan ya lashe zaben shugabancin kasar.