(ABNA24.com) Kungiyar tarayyar Afirka ta bada sanarwan cewa an warware kasha 90% na sabanin da ke tsakanin kasashen Masar, Sudan da Habasha dangane da matsar ruwa ta Renaissance.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik nakalto shugaban kungiyar Musa Faki Mohammad yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa kungiyar tare da wakilan kasashen uku, wato Sudan, Masar da Habasha sun cimma yarjejeniya a tsakaninsu dangane da madatsar ruwa kan kogin nilu wacce suke takaddama a kanta tun fiye da shekaru 10 da suka gabata.
Har’ila yau Labarin ya nakalto Bisam Radhi kakakin fadar shugaban kasar Masar yana cewa a wani taro tsakanin shuwagabannin kasashen uku, tare da tawagar shuwagabanni na kungiyar tarayyar Afrika inda suka warware matsalar a matakin farko dangane dangane da madatsar ruwan.
Kasar Habasha ta fara gina madatsar ruwa na Renaissance ne a shekara ta 2011, da fatan za ta fara amfani da ita a shekara ta 2017, amma saboda sabani tsakanin kasashen uku an jirkirta fara amfani da madatsan ruwa.
/129
28 Yuni 2020 - 06:51
Lambar labari: 1050902
Kungiyar tarayyar Afirka ta bada sanarwan cewa an warware kasha 90% na sabanin da ke tsakanin kasashen Masar, Sudan da Habasha dangane da matsar ruwa ta Renaissance.