(ABNA24.com) Shugaban Najeria Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga shugabancin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Kudu-Maso-Kudu, Victor Giadom.
Mai magana da yawun shugaban kasar ne Garba Shehu ya sanar da haka a takarda da ya fitar ranar jiya Laraba.
Garba Shehu ya ce; “ Buhari zai halarci taron jam’iyyar APC wanda Giadom ya kira, saboda shi ne shugaban jam’iyyar a halin yanzu, kamar yadda kotu ta yanke hukunci.”
Ya kara da cewa; “ Kwararru sun ba shugaba Buhari shawara game da badakalar shugabancin jam’iyyar, kuma yabi wannan shawara, inda a karshe dai hankalinsa ya fi kwanciya kan shugabancin Giadom a matsayin shugaban jam’iyyar na wucin gadi bisa hukuncin kotu.
Kamar yadda Garba Shehu ya fadi, ana sa ran shugabannin jam’iyyar, gwamnoni da ‘yan majalisu za su halarci wannan taro.
Kotu ta yanke hukunci kan cewa Giadom ne shugaban jam’iyyar na tsawon makonni biyu masu zuwa, amma kuma jam’iyyar ta garzaya kotu, inda ita ma bukaci kotu ta bayar da izinin jingine hukuncin waccan kotun.
Giadom dai ya tsaya kai da fata a kan cewa shi ne shugaban jam’iyyar APC a yanzu.
Kotun daukaka kara ta dakatar da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole daga jam’iyyar a dalilin hukuncin dakatar da shi da kotu ta yi a baya.
/129
25 Yuni 2020 - 07:23
Lambar labari: 1050110
Shugaban Najeria Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga shugabancin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Kudu-Maso-Kudu, Victor Giadom.