(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa Iran tana fama da mummunan halin tattalin arziki, amma ya na da tabbaci kan cewa nan ba da dadewa ba, za’a fita daga wannan halin.
Tashar talabijin ta Al-alam wacce take watsa shirye-shiryenta da harshen Larabaci a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar yana fadar haka a yau Talata a lokacinda yake jawabi a taron kwamitin tattalin arzikin kasar a nan birnin Tehran.
Shugaban ya kara da cewa yana fatan a duk lokacinda kudaden kasar daga kasashen waje suka shigo, ana iya warware matsalolin da ke faruwa a kasuwar musayan kudade na kasar a Halin yanzu.
Daga karshe shugaba Rouhani ya bukaci hadin kai tsakanin ma’aikatun kasar da kuma sauran mutanen kasa, don ganin bayan mummunan halin tattalin arziki wanda kasar ta ke ciki sanadiyyar takunkuman tattalin arzikin masu tsanani, wadanda makiya kasar suka dora mata.
/129
24 Yuni 2020 - 07:19
Lambar labari: 1049743
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa Iran tana fama da mummunan halin tattalin arziki, amma ya na da tabbaci kan cewa nan ba da dadewa ba, za’a fita daga wannan halin.