14 Yuni 2020 - 09:46
Mutum 42 Sun Raunana A Zanga-Zangar Lebanon

Fada tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro a wasu birane a kasar Lebanon ya kai ga raunata mutane akalla 42 a jiya Jumma’a.

(ABNA24.com) Fada tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro a wasu birane a kasar Lebanon ya kai ga raunata mutane akalla 42 a jiya Jumma’a.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da zanga-zangar ne don nuna damuwa ga faduwar darajar kudaden kasar wanda ake kira Lira idan an kwatanta da dalar Amurka.

Faduwar darajar kudaden ya jefa rayuwar mutanen kasar, musamman talakwa cikin kunci, da wahala. A birnin Tripoli dai masu zanga-zangar sun kona langunan zuma shara na kan titi, da kuma rufe titunan da tayoyi wadanda suka sanyawa wuta.

Jami’an tsaro sun yi kokarin tarwatsa su ta hanyar jefa masu borkokon tsohuwa.

Kimani watannin 8 da suka gabata ne aka fara zanga-zanga a kasar Lebanon wanda ya kai ga saukar firai ministan kasar daga mukaminsa.

Amma duk da cewa an kafa sabuwar gwamnati har yanzun darajar kudaden kasar suna dada faduwa wanda ya tilastawa mutanen kasar sake fitowa kan tituna.


/129