14 Yuni 2020 - 09:15
Alkazimi:Ayatullahi Sistani Ya Bata Makircin Kungiyar Daesh Na Wargaza Kasar Iraqi

Firai ministan kasar Iraqi Mustafa Alkazimi ya bayyana fatawar jihadi wacce Ayatullahi Ali Sistani ya fitar ne ta kubutar da kasar Iraqi daga mamayar kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh.

(ABNA24.com) Firai ministan kasar Iraqi Mustafa Alkazimi ya bayyana fatawar jihadi wacce Ayatullahi Ali Sistani ya fitar ne ta kubutar da kasar Iraqi daga mamayar kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh.

Majiyar muryar JMI ta nakalto firai ministan yana fadar haka a jiya Asabar, ranar da aka cika shekaru 6 cur da kafa dakarun Hashdushaabi a shekara ta 2014 bayan da kungiyar Daesh ta mamaye yankuna masu yawa a kasar ta Iraqi.

Fatawar babban marja’in wacce ta bayyana yakar kungiyar Daesh a matsayin jihadi kan tafarkin All.. kuma wajibin kifaya ne kan mutanen kasar Iraqi su yi hakan.

Dakarun hashdushabi dai, wacce ta hada bangarorin kasar Iraqi daban-daban, wadanda suka hada da Masulmi shia’a da Sunnan suna da babban tasiri wajen karya lagon kungiyar Daesh a kasar ta Iraqi.

Sannna a halin yanzu dakarun suna aiki kafada da kafada da sojojin kasar Iraqi don kawo karshen ragiwar mayakan na Daesh a kasar ta Iraqi.


/129