14 Yuni 2020 - 09:15
Iran, Rasha Da Turkiyya Zasu Tattauna Kan Rikicin Siriya

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani, da tokwarorinsa na kasashen Rasha ta Turkiyya za su gudanar da taro dangane da rikicin kasar Siriya karkashin yarjejeniyar Astana.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani, da tokwarorinsa na kasashen Rasha ta Turkiyya za su gudanar da taro dangane da rikicin kasar Siriya karkashin yarjejeniyar Astana.

Jaridar Tehran times ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Turkiya Mevlut Cavusoglu yana fadar haka a ranar Alhamis, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Iran ce ya kamata ta shirya wannan taron a wannan karon, amma saboda yaduwar cutar Corona a halin yanzu za’a gudanar da taron ta kafar bidiyo ne.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin kasashen Turkiya da Rasha a shirye suke su halarci taron, amma suna jiran Iran wacce zata jagoranci taron ta bayyana ranar da za’a gudanar da shi.

An fara tarurrukan zaman lafiya a kasar Siriya na Astana ne a shekara ta 2017 tsalanin kasashen ukku, wannan shi ne taro na 5 sannan babbar manufar tarurrukan sun hada da kawo bangarorin da suke yakar juna a kasar Siriya zuwa kan teburin tattaunawa, tsagaita budewa juna wuta, samar da tallafi ga ‘yan gudun hijirar kasar, shirin dawowan ‘yan gudun hijira gidajensu da kuma sake gina kasar ta Siriya.

Har’ila yau an bukaci kasashen waje su daina katsalanda cikin rikicin kasar ta Siriya sannan su taimaka wajen samar da sabon kundin tsarin mulkin kasa wanda ‘yan kasar zasu rubuta su kuma amince da shi.


/129