8 Yuni 2020 - 06:12
WHO : A Rika Amfani Da Takunkumin Rufe Fuska Domin Dakile COVID-19

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sabunta ka'idojinta na amfani da takunkumin rufe baki da hanci wajen dakile yaduwar COVID-19, inda ta shawarci jama'a, su rika sanya takunkumin a inda ba za su iya kaucewa taron jama'a ba.

(ABNA24.com) Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sabunta ka'idojinta na amfani da takunkumin rufe baki da hanci wajen dakile yaduwar COVID-19, inda ta shawarci jama'a, su rika sanya takunkumin a inda ba za su iya kaucewa taron jama'a ba.

Darektan hukumar ta WHO, Tedros Adhnom Ghebreyesus, ya bukaci gwamnatoci su karfafawa al'ummu gwiwar sanya takunkumin na baki da hanci a inda ake samun yaduwar cutar da wuraren taron jama'a.

Sai dai, hukumar ta yi gargadin cewa, sanya takunkumin ba ya nufin maye gurbin matakin nisantar jama'a, ko tsaftar hannu ko sauran wasu matakan da ake dauka don dakile cutar, ta na mai cewa, takunkumin na da muhimmanci a matsayin wani bangare na dabarun yaki da COVID-19.



/129