8 Yuni 2020 - 06:12
Mali: Mutane 26 Sun Rasa Rayukansu A Yankin Mopti

Wani Harin Wuce Gona Da Iri Ya Lashe Rayukan Mutane 26 A Yankin Mopti Da Ke Tsakiyar Kasar Mali

(ABNA24.com) Mahukunta a kasar Mali sun bayyana cewa: Wani gungun mahara sun kai farmaki kan kauyen Fulani mai suna Binedama a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar Mali a ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka kashe mutane 26 tare da kona kauyen.

Wani jami’in karamar hukumar Koro da ke makobtaka da yankin na Mopti ya bayyana cewa: Maharan sun kaddamar da farmaki kan kauyen na Binedama ne a tsakiyar ranar Juma’a, inda suka kashe mutane akalla 26 ciki har da mata biyu da wata yarinya ‘yar shekaru 9 a duniya.

Yankin Mopti da ke tsakiyar kasar Mali ya yi kaurin suna wajen samun tashe-tashen hankula da ke da alaka da kabilanci tsakanin Fulani makiyaya da ‘yan kabilar Dogon da suka shahara da noma da farauta, hasarar rayuka mafi muni ita ce harin wuce gona da iri da aka kai kan ‘yan kabilar Dogon, inda aka kashe mutane 95 a watan Yunin shekarar da ta gabata.



/129