5 Yuni 2020 - 15:09
Bankin Ci Gaban Afrika, Zai Gudanar Da Sabon Binkicen Rashawa Kan Shugabansa

Bankin ci gaban Afirka, ya sanar da kaddamar da sabon bincike mai zaman kansa kan shugaban bankin, Akinwumi Adesina, a kan zarge-zargen cin hanci da karbar rashawa.

(ABNA24.com) Wannan na zuwa ne mako guda bayan da hukumar gudanarwar bankin na AfDB, ta wanke M. Adesina daga zargin nuna bangaranci.

An dai jima ana zargin shugaban bankin, Akinwumi Adesina, wanda tsohon ministan aikin gona na Najeriya ne da nada 'yan uwansa a kan wasu manyan mukamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa, sai dai Mr Adesina ya musanta zarge-zargen.

342/