28 Mayu 2020 - 05:24
Kenya : Ana Neman Mutum 400 Don Gwajin Riga Kafin Korona

Masu bincike kan magunguna a Kasar Kenya na neman mutum 400 domin gwajin wani maganin alurar riga kafin cutar korona akansu.

(ABNA24.com) Masu bincike kan magunguna a Kasar Kenya na neman mutum 400 domin gwajin wani maganin alurar riga kafin cutar korona akansu.

Ana son yin gwajin maganin ne kan ma’aikatan lafiya mazauna yankunan Mombasa da kuma Kikifi.

Maganin wanda jami’ar Oxford, ta samar mai suna ChAdOx1 nCoV-19, dama an riga an gwada shi kan mutum sama da 1,000 guda a Biritaniya.

A cen baya dai gudanar da gwajin maganin cutar korona a Afrika, ya tayar da zazzafar muhawara, saidai wannan karo masana sun ce za’a bi ka’ida kafin guidanar da duk wani gwaji.


/129