26 Mayu 2020 - 06:54
​An Fara Sauke Kayan Da Iran Ta Aike Zuwa Kasar Venezuela

Jakadan kasar Iran a birnin Carakas ya ce, an fara sauke kayan da jiragen ruwan kasar Iran suke dauke da su a gabar ruwan kasar Venezuela.

(ABNA24.com) Jakadan kasar Iran a birnin Carakas ya ce, an fara sauke kayan da jiragen ruwan kasar Iran suke dauke da su a gabar ruwan kasar Venezuela.

A zantarwasa da tashar alalam daren jiya, jakadan Iran a kasar Vezezuela Hojjatollah Sultani ya bayyana cewa, a halin yanzu manyan jiragen ruwan Iran guda biyu sun isa gabar ruwan kasar Venezuela, kuma tuni an fara sauke kayan da suke dauke da su, kuma guda uku suna kan hanyar isa kasar ta Venuela yanzu haka.

Sultani ya ce; dukkanin jiragen suna dauke da kayayyaki da suka hada tataccen man fetur, da dangoginsu, sai kuma kayayyakin gyaran matatun mai, wadanda kasar Venezuela take da matukar bukatuwa zuwa gare su, amma kuma ba za ta iya shigo da su ba, saboda takunkumin da Amurka ta kakaba mata kan hakan.

Ya ci gaba da cewa, babu wata matsala da jiragen na Iran suka samu a kan hanaya, domin kuwa hakan bai sabawa wata doka ta duniya ba, ko da hakan ya sabawa takunkumin Amurka, amma a cewarsa, takunkumin Amurka ba doka ce ta duniya ba.

Ya kara da cewa, babu gaskiya a rahotannin da wasu kafofin yada labarai suke watsawa, kan cewa Venezuela ta bayar da zinariya ton 9 ga Iran, domin aike mata da wadannan kayayyaki.


/129