(ABNA24.com) Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan halakar wani sojan kasar sanadiyyar raunin da ya samu daga dotsen da wani bafalasdine ya jefa a kansa a jiya Litinin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sojan da ya halakan yana daga cikin sojojin da aka tura don kama wasu falasdinawa 4 wadanda yahudawan suke tuhuma da ayyukan ta’addanci a garin Ya’bah na yankin yamma da kogin Jordan a jiya.
Labarin ya kara da cewa Sergeant Amit Ygal dan shekara 21 a duniya ya hadu da ajalinsa ne a lokacinda wani ba falasdine wanda yake kan wani gini ya jefa dutse a kan goshinsa ya kuma zama sanadiyyar halakarsa.
Majiyar yahudawan ta kara da cewa an fara bincike kan mutuwar sojon, da kuma ganin an kama falasdinen da ya kasheshi.
Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu dai yana kokarin karbe iko da yankin yamma da kogin Jordan saboda tabbatar da goyon bayan da shugaban kasar Amurka ya bashi na ya yin hakan a cikin abinda suka kira “Yarjejeniyar Karni” ta kara kwace yankunan falasdinawa.
/129*
13 Mayu 2020 - 06:20
Lambar labari: 1036349
Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan halakar wani sojan kasar sanadiyyar raunin da ya samu daga dotsen da wani bafalasdine ya jefa a kansa a jiya Litinin.