(ABNA24.com) A Rwanda mutane 72 ne, aka rawaito cewa sun rasa rayunkansu, kana wasu hudu sun bata, yayin wata zabtarewar kasa da kuma ambaliyar ruwa da aka fuskanta a kasar.
Lamarin ya biyo bayan ruwan sama da aka tabka a yankunan arewaci da kuma yammacin kasar a makon da ya gabata.
Iftila’in ya raba daruruwan iyalai da muhalllansu, da lalata sama da eka 200 na filayen noma, kamar yadda ma’aikatar kula da agajin gaggawa ta kasar Rwandar ta sanar.
An dai shafe tsawon watanni ba’a fuskanci irin hakan ba a kasar, duk da cewa Rwandar na fama da irin wannan iftila’in a lokutan damana.
/129