(ABNA24.com) Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, tun da jijjifin safiyar yau ne makaman atilare na dakarun haftar suka fara harba manyan makamai a kan filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Tripoli, kuma har zuwa wannan lokaci harin na ci gaba.
Wadannan hare-hare dai na zuwa kawana daya bayan harin da dakarun gwamnatin Triploi suka kadammar ne da jirage marassa matuki da ake sa ran na sojojin Turkiya ne a kan garin Rajban da ke karkashin dakarun Haftar, inda gwamnatin Tripoli ta ce ta kashe wasu daga cikin dakarun Haftar.
Baya ga haka kuma jiragen yakin marassa matuki na gwamnatin Tripoli sun kai wasu hare-haren a garin Zantan, wanda rabinsa yake hannun dakarun Haftar, rabi kuma yake hannun dakaru masu biyayya ga Tripoli.
/129
10 Mayu 2020 - 05:17
Lambar labari: 1035213
Dakarun Khalifa Haftar suna ci gaba da yin luguden wuta a kan birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya.