(ABNA24.com) Bayan shafe kusan makwanni hudu na kafa dokokin suka jibanci dakile yaduwar annobar coronavirus, wasu kasashen Afrika, sun fara sassauta dokar kulle.
A Lesotho, kasa daya tilo inda cutar bata yadu ba, yau Laraba ne aka dage dokar kulle.
A Burkina Faso, kuwa a jiya Talata ne aka dage dokar killace birane 12 da aka kafa domin dakile yaduwar annobar.
A Najeriya, kuma ranar Litini ne aka fara sassauta dokar kulle sakamakon annobar coronavirus a jihohin Legos da kuma Abuja, babban birnin tarayya a wani mataki na ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa.
A cen kuwa Afrika ta Kudu, tun a ranar Juma’a data gabata ne aka koma bakin aiki.
Ye zuwa jiya Talata, mutane dubu 47, 581 aka tabbatar sun harbu da cutar coronavirus a Afrika.
Adadin kuma wadanda cutar ta yi ajalinsu kawo yanzu ya kai 1,862 a fadin nahiyar, kamar yadda hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kungiyar tarayyar AFrika ta sanar.
Kasashen dake sahun gaba sun hada da Afrika ta Kudu, mai mutanen da suka harbu da cutar 7,220, sai Masar, mai mutum 6813, cen kuma akwai kasashen dake biye musu da suka hada da Morocco, Ajeriya, Najeriya da kuma Ghana.
/129
7 Mayu 2020 - 04:31
Lambar labari: 1034338
Bayan shafe kusan makwanni hudu na kafa dokokin suka jibanci dakile yaduwar annobar coronavirus, wasu kasashen Afrika, sun fara sassauta dokar kulle.