(ABNA24.com) Jaridar ‘Annashrah’ ta nakalto majiyar sojojin kasar ta Lebanon tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar dangane da rikici tsakanin masu Zanga-zangar nuna damuwarsu da yadda tattalin arzikin kasar ya tabarbare, da kuma sojojin kasar.
Labarin ya kara da cewa masu Zanga-zanga a birnin Tripoli daga arewacin kasar sun yi amfani da duwatsi, abubuwa masu fashewa kirar hannu kan sojojin kasar wanda ya kai ga raunata da dama daga cikinsu.
Labarin ya kara da cewa masu Zanga-zangar sun lalata dukiyoyin jama’a da dama a birnin Tripoli, sannan daga ranar Litinin da aka fara Zanga-zangar zuwa yau sojoji akalla 40 ne suka ji rauni a birnin Tripoli kadai.
Firai ministan kasar ta Lebanon Hassan Diyab ya dora laifin tashe-tashen hankula na baya-bayannan kan wasu ‘yan siyasa wadanda suke son cimma wasu manufofinsu a kasar.
/129
2 Mayu 2020 - 03:42
Lambar labari: 1032220
Majiyar sojojin kasar Lebanon ta bayar da sanarwa cewa an ji wa sojojin kasar kimanin 23 rauni a rikicin daren larabar da ta gabata kadai.