(ABNA24.com) A Isra’ila dubban masu zanga zanga ne suka fito kan tituna a birnin Tel-aviv domin nuna kin amincewarsu da yarjejeniyar kafa gwmanati tsakanin Benjamin Netanyahu da tsohon abokin hammayarsa Benny Gantz.
Bayanai sun ce duk da barazanar annobar coronavirus hakan bai hana masu zanga zangar fitowa ba domin bayyana kin amincewarsu da yarjejeniyar kafa gwamnatin wacce a cewarsu ke barazana wa tsarin demokuradiyya.
Masu zanga zangar na ganin babu wata tsayayar demokuradiyya da za’a samar tare da Netamyahu wanda aka tuhuma da cin hanci da rashawa.
A ranar Litini data gabata ce Benjamin Netanyahu na jam’iyyar Likoud da kuma abokin hammayarsa Benny Gantz, na jam’iyyar da ake wa lakabi da launin shudi da fari suka amince kafa gwamnatin hadaka bayan shafe watanni 16 na dambarwar siyasa.
Yarjejeniyar dai ta tanadi Benjamin Natanyahu wanda aka dage shari’arsa kan cin hanci da rashawa, ya sake rike mukamin firai minista har na tsawan watanni 18, bayan hakan sai abokin hammayarsa Benny Gantz, ya karbi mukamin.
/129
26 Afirilu 2020 - 06:16
Lambar labari: 1029862
A Isra’ila dubban masu zanga zanga ne suka fito kan tituna a birnin Tel-aviv domin nuna kin amincewarsu da yarjejeniyar kafa gwmanati tsakanin Benjamin Netanyahu da tsohon abokin hammayarsa Benny Gantz.