(ABNA24.com) Alkalumma da hukumomin kiwan lafiya na kasar suka fitar a jiya Asabar sun kuma ce adadin mutanen da cutar ta kashe ya kai 27 bayan sasun mutum uku da cutar ta yi ajalinsu.
Wadanda suka samu warkewa daga cutar kuma sun kai 325.
Hukumomin kasar dai na ci gaba da kira ga jama’a su kiyaye matakan kare kai daga kamuwa da cutar, da suka hada da sanya takunkumin rufe baki da hanci da kuma kauracewa taruwar jama’a.
/129
26 Afirilu 2020 - 06:15
Lambar labari: 1029860
A Jamhuriyar Nijar, adadin mutanen da suka harbu da cutar coronavirus, ya haura zuwa 684, bayan gano wasu mutum 3 da suka kamu.