22 Afirilu 2020 - 05:29
Iran Ta Ce; Takunkuman Da Amurka Ta Kakaba Mata Sun Mayar Da Ita Mai Jurewa Faduwar Farashin Man Fetur

Mataimakin shugaban kasar Iran, Ishak Jahangir ne ya bayyana hakan, sannan ya kara da cewa; babu wata kasa a duniyar nan hatta wacce tattalin arzikinta yake bunkasa da kaso 25%, da za ta tsira daga mummunan tasirin cutar corona.

(ABNA24.com) Mataimakin shugaban kasar Iran, Ishak Jahangir ne ya bayyana hakan, sannan ya kara da cewa; babu wata kasa a duniyar nan hatta wacce tattalin arzikinta yake bunkasa da kaso 25%, da za ta tsira daga mummunan tasirin cutar corona.

Jihagir ya kara da cewa; Tabbas kasashe masu albarkatun man fetur kamar Saudiyya za su fuskanci matsalar tattalin arziki.

Farashin man fetur ya fadi kasa warwas saboda koma bayan nemansa da ake yi a kasuwannin duniya sanadiyyar bullar cutar corona.

A ranar Litinin din da ta gabata farashin man fetur din ya yi wata irin faduwa a kasuwannin Amurka ta yadda ya kai kasa da sifiri akan kowace ganga, kafin a jiya Talata farashin gangar ya koma dala 4.29


/129