(ABNA24.com) An gudanar da zaben duk da barazanar annobar coronavirus, da matsalar tsaro, da kuma ci gaba da garkuwa da madugun ‘yan adawa na kasar.
Tunda farko dai an nuna fargaba akan samun fitowar jama’a sosai a zaben.
Ana sa ran samun bayannan farko farko na sakamakon zaben a farkon makon gobe.
A ranar 20 ga watan Maris da ya gabata ne aka gudanar da zagayen farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar wanda a cen baya aka sha dagewa saboda dalilai na tsaro masu nasaba da rikice rikicen kabilanci tawaye da barazanar mayakan dake ikirari da sunan jihadi.
/129
20 Afirilu 2020 - 06:32
Lambar labari: 1027634
A Mali, ‘yan kasar ne suka kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar zagaye na biyu da aka gudanar a yau Lahadi.