(ABNA24.com) Rahotanni daga kasar Libya na cewa, a yau dakarun gwamnatin Tripoli sun kaddamar da wasu hare-hare a kan garin Sarman da ke yammacin birnin na Tripoli.
Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, tun da jijjifin safiyar yau Litinin ne dakarun gwamnatin Tripoli suka fara kaddamar da hare-hare a kan garin Sarman, wanda dakarun Haftar suke iko da shi.
Rahoton ya ce wannan harin na zuwa ne bayan sanar da kakkabo jiragen yaki biyu mallakin rundunar Haftar da suka kai hari kan Tripoli a jiya.
Haka na kuma jiragen yakin gwamnatin Tripoli sun kai wasu hare-hare kan dakarun Haftar a garin Sabrata da ke yammacin kasar ta Libya, wanda ya yi sanadiyyar kashe biyu daga cikin dakarun Haftar.
Rikicin kasar ta Libya ya kara tsananta ne a cikin wannan mako, bayan da dakarun Haftar suka kara matsa kaimi a yunkurinsu na kwace iko da birnin Tripoli, yayin da gwamnatin Tripoli ta sanar da cewa ta shirya yin yaki na tsawon lokaci tsakaninta da Haftar.
/129
14 Afirilu 2020 - 05:53
Lambar labari: 1025440
Rahotanni daga kasar Libya na cewa, a yau dakarun gwamnatin Tripoli sun kaddamar da wasu hare-hare a kan garin Sarman da ke yammacin birnin na Tripoli.